A yayin da ake gab da fara muhimman ayyukan ibada a hajjin bana, hukumar Alhazan Najeriya ta ce ta shirya tsab tun tinkarar duk wata matsala da ka taso saboda alhazan Najeriya wajen dubu 80 su samu gudanar da ayyukan ibada cikin natsuwa.
Alhazan Najeriya, kamar sauran alhazai daga sassan duniya su wajen miliyan biyu, sun kama hanyar zuwa Muna don fara muhimmin fanni na aikin na haji, na samun kulawa sosai a cewar Abdullahi Salame, Shugaban Kwamitin Wakilai da ya sa ido kan shirin aikin hajjin na bana. Ya ce an tanadar ma kowane alhaji abin sanyaya masa yanayi kuma an samar da motoci masu na’urar sanyaya wuri.
Baya ga sauran abubuwan kyautata aikin hajjin na bana, an kuma ba da bangaren lafiyar maniyyata muhimmnaci. Dr. Ibrahim Kana, mai kula da bangaren lafiyar mahajjata, ya ce baya ga tanada isassun magunguna, an kuma raba ma’aikatan jinya zuwa jahoji saboda a samar da cikakkiyar kulawa.
Ga Madina Dauda da cikakken labarin:
Your browser doesn’t support HTML5