Afirka: Tarayyar Turai Zata Bada Tallafi Domin Dakile Kwararar 'Yan Nahiyar Zuwa Turai

Taron shugabannin kasashen tarayyar Turai da na kasashen Afirka

Kungiyar tarayyar Turai ta amince ta baiwa Africa dala biliyan 2 domin magance matsalar talauci da kuma kwararan yan nahiyar zuwa kasashen yammacin turai.

Kungiyar tace yin hakan zai bunkasa tattalin arzikin nahiyar da matsalar tsaro da samar wa yan nahiyar damar walwala.wannan dai duk yana zuwa ne a karshen taron da shugabannin kungiyar tayi da shugabanin Africa.

Haka kuma Shugaban Jamus Angela Markel tace zasu kara yin wani taro da shugabannin na Africa a cikin karshen wannan watan ko kuma a farkon watan gobe a Turkiyya, domin duba yadda za a shawo kan matsalar kwararan yan Africa zuwa nahiyar Turai.

Sai dai kuma Turkiyya tana ganin kokarin da kaashen Jamus,Sweden,Slovenia da wasu kasashen dake cikin kungiyar tarayyar Turan na zamowa wata barazana ga bakin iyakar ta, musammam daga dubun dubatan yan gudun huijiran dake neman mafaka da suka fito daga Africa ta tsakiya, Africa, da kuma Asiya.