Afirka Ta Kudu ta janye Jakadanta daga kasar Isira’ila jiya Talata, bayan da sojojin Isira’ila su ka kashe 60 daga cikin Falasdinawan da ke zanga-zanga akan bude ofishin Jakadancin Amurka a birnin Kudus da ake takaddama a kai.
Sashin Harkokin Cudanyar Kasa da Kasa da Hadin Kai ya yi Allah wadai da matakin da sojojin Isira’ila suka dauka game da Falasdinawan da ke zanga-zanga a Gaza, da cewa, “Wadanda abin ya rutsa da su na zanga-zangar lumana ne kan takalar da Amurka ta yi, ta wajen kaddamar da Ofishin jakadancinta a Birnin Kudus.”
Wannan tashin hankalin, a cewar Sashin, ya sa Afirka ta Kudu ta gaggauta janye jakadanta daga Tel Aviv, inda akasarin Ofisoshin Jakadancin kasashe su ke a kasar Isira’ila.
Masu zanga-zangar, wadanda yawansu na saye da riguna masu dauke da sakon da ke cewa, “A ‘Yantar da Falasdinu” da kuma wanda ke cewa, “A Tsai Da Manufofin Wariya Na Isira’ila” --- ciki har da wata ‘yar kungiyar mutanen da ke kiran kansu Yahudawan Afirka Ta Kudu ‘Yan Rajin ‘Yantar da Falasdinawa.