Sanarwar ta kara da cewa, an sayar da rukunin da abin ya shafa a kasashen Afirka ta Kudu da Eswatini da Rwanda da Kenya da Tanzania da kuma Najeriya.
Janyewar ta biyo bayan rahoton da takwarar aikin hukumar a Najeriya ta bayar a ranar Laraba, wadda ta fara gano gubar a cikin wani nau'in ruwan maganin na Benylin na yara.
Idan ba a manta ba, kasashen Kenya da Najeriya ne suka fitar da janyewar maganin wanda ake amfani da shi wajen maganin zazzabi da sauran matsalolin da ke shafar numfashin.
Ku Duba Wannan Ma Najeriya Ta Janye Maganin Tarin Yara Na J&J Daga Kasuwa Saboda IllaKenvue (KVUE.N), wanda a yanzu ya mallaki Benylin bayan da J&J bangaren maganin ya balle bara, ya fada a wata sanarwa cewa yana gudanar da nasa gwaje-gwajen tare da yin aiki da hukumomin lafiya don sanin matakin da za a dauka.
"Bita na bayanan bayanan na kariyar lafiyarmu na duniya na tsawon lokacin da aka saki samfurin a watan Mayu 2021 zuwa 11 ga Afrilu 2024 bai gano wata guba ba ga kowane rukuni na Benylin Pediatric Syrup," in ji shi.
An danganta yawan sinadarin diethylene glycol fiye da misali a cikin maganin tari da mutuwar yara da dama a Gambia, Uzbekistan da Kamaru tun daga shekarar 2022 a daya daga cikin mace-macen guba mafiya muni a duniya.