A Afirka ta kudu shugaba Jacob Zuma, wanda yake fama da koma baya ta fuskar zabe da bai taba ganin irinta ba a zabukan kananan hukumomi, yace masu zabe "suna aikewa da sakonni ta ko wani fanni," saboda haka yace jam'iyyarsa ta ANC zata kasa kunne sosai ta saurare su."
Shugaba Zuma yayi magana ne Asabar, yayinda sakamakon zabe yake nuna jam'iyyar ta ANC mai mulkin kasar ta fadi zabe a babban birnin kasar Pretoria, hakanan jam'iyyar ta rasa rinjaye a cibiyar kasuwancin kasar birni mafi girma Johannesberg.
Tuni jam'iyyar marigayi Nelson Mandela ta amince ta fadi zabe a birnin da ake kira Port Elizabeth ranar jumma'a da kusan kashi 7 cikin dari.
A sassan kananan hukumomi ciki harda Pretoria, jam'iyyar DAP mai hamayya ta sami kashi 43.1 na kuri'u da aka kada,yayinda jam'iyyar ANC ta sami kashi 41.2
Kuri'ar neman jin ra'ayin jama'a ta nuna cewa a fadin kasar har yanzu jam'iyyar ANC take kan gaba da maki 54 cikin dari. Duk da haka wadannan alkaluma ba zasu kwantarwa jam'iyyar hankali ba,ganin sakamakon zabe a jiya Asabar, ya nun jam'iyar zata rasa rinjaye da take da shi har sai ta bukaci hada kai da wasu jam'iyu idan har zata ci gaba da shugabanci a birnin.
Shugaba Zuma yana fama da abun fallasa tun bayan a ya kama aiki shekaru bakawai da suka wuce.A wani lamari an same shi da laifin amfani da kudin gwanati dala dubu dari biyar wajen gyara gidansa. Kotun tsarin mulkin kasar ta bukaci ya biya gwamnati wadnanan kudade.