Jami’ai a Afghanistan sun ce akalla mutum 32 ne suka mutu kana aka raunata wasu 60, bayan da wasu ‘yan bindiga suka bude wuta a wajen wani taro da ya samu halartar manyan ‘yan siyasar bangaren adawa a Kabul.
Shaidu sun ce maharan sun bude wuta ne a daidai lokacin da tsohon mataimakin shugaban kasar Karim Khalili yake gabatar da jawabinsa a wajen taron.
An shirya taron ne domin tunawa da mutuwar wani fitaccen dan siyasar kabilar Hazara na bangaren ‘yan Shi’a marasa rinjaye.
Taron wanda ake nuna shi kai-tsaye ta talabijin, ya nuna lokacin da Khalili da ke jawabi ya arce yana neman mafaka tare da wasu jama’a, a lokacin da maharan suka bude wuta daga wani gida da ake kan ginawa.
Rahotanni sun ce daga cikin wadanda suka mutu har da mata da kananan yara,.
Ana kuma kuma nuna fargabar mai yiwuwa adadin wadanda suka mutun zai karu.
Sai dai ma’aikatar cikin gida a Afghanistan ta ce, jami’an tsaron kasar sun yi artabu da ‘yan bindigar sun kuma kashe su.