Jami’ai a Afghanistan sun ce wani sabon hari da aka kai a yankin da ake gabzawa na gabashin kasar ya kashe kimanin ‘Yan tsagerun kungiyar ISIS 34 ya kuma ragargaza gidan radiyon ‘Yan Tsagerun wanda suke amfani dashi wajen yada Farfaganda.
Ministan Cikin gida na Afghanistan ya fada a yau Litinin cewa amn auna harin ne a wata maboyar ‘Yan IS dake Naziyan da kuma gundumar Achin a Yankin Nangarhar, dake da iyaka da Pakistan.
A bayanin da Ministan ya bayar yace “Tashar gidan radiyon tana watsa labarai ne ta haramtacciyar hanya a yankin na Nangarhar, suna yada sakonnin kungiyar na tsatstsauran ra’ayi da kuma barazana ga mutane da kuma jami’an gwamnati.”