Afghanistan da Pakistan sun tattauna akan samun zaman lafiya

Prime Ministan Pakistan da shugaban kasar Afghanistan

A wani yunkurin sausauta zaman tankiya ko kuma zaman dar dar akan caje cajen ta'adanci da kuma gano hanyoyin inganta yunkurin samun zaman lafiya na Afghanistan, jiya Juma'a shugaban kasar Afghanistan da wani baban jami'in Pakistan makwapciyarta suka yi shawarwari a birnin Kabul.

A wani yunkurin sausauta zaman tankiya ko kuma zaman dar dar akan caje cajen ta'adanci da kuma gano hanyoyin inganta yunkurin samun zaman lafiya a Afghanistan, jiya Juma'a shugaban kasar Afghanistan da wani baban jami'in Pakistan makwapciyarta suka yi shawarwari a birnin Kabul.


Babu wani bayani da aka gabatar akan wannan tozali da aka yi tsakanin shugaba Ashraf Ghani da kuma mai baiwa gwamnatin Pakistan shawarwari akan matakan tsaron cikin gida Sartaj Aziz. Jami'an biyu sun gana ne a gefen taron kungiyar hadin kan tattalin arzikin yankin da ake yi akan kasar Afghanistan.

Ana kuma yin taron ne a yayinda Afghanistan ke guna gunin cewa Pakistan ta kasa daukan wani matakin akan yan kungiyar Taliban da yan tawayen da aka danganta da kungiyar Haqqani da aka yi zargin cewa suna gudanar da hidimominsu ne daga bangaren kan iyakar Pakistan

.
Kafofin gwamnati sunce anyi tattaunawar awa daya da mintoci talatin tsakanin kasashen biyu, to amma kuma basu fadi ba dada ko shawarwarin sun taimaka wajen tinkarar batutuwan dake damun kasashen biyu

.
Bayan ganawar shugaba Ghani ya yiwa mahalarta taron bayanin cewa tun lokacinda ya dare kan ragamar mulki, gwamnatinsa ta yi kokarin yin shawarwari da yan tawaye tare da shiga tsakanin Pakistan, to amma kuma yana nuna tababa gameda yunkurin da Pakistan ke yi.


Shugaban na Afghanistan bai bada wani karin haske ba, amma kasar sa ta dade tana zargin rundunar sojan Pakistan da laifin goyon bayan yan Taliban a Afghanistan da kuma yin shishigi a harkokin kasar sa.