Afghanistan Ta Nemi Pakistan Ta Bude Mashigin Da Ta Rufe

Kan iyakokin Afghanistan da Pakistan

Afghanistan ta yi amfani da babban taron kolin yankin ta yi kira ga kasar Pakistan da ta sake bude iyakar dake ratsawa tsakanin kasashen biyu a hukumance.

Hakan zai kawar da shingayen cinikayya da kuma cire umurnin hana kai da komon jama’a, tare da habbaka ayyukan raya tattalin arziki tsakanin kasashen yankin.

Pakistan da ta dauki bakuncin taron kolin na yau Laraba tsakanin kungiyar raya tattalin arziki ta kasashe goma na yankin ko kuma ECO a takaice, ta rufe kan iyakokinta makwanni biyu da suka wuce, ta na zargin cewa akwai ‘yan ta’adda da suka shirya kai hare-hare daga Afgahnistan.

Firai ministan Pakistan Nawaz Sharif ne ya jagoranci taron da shugabannin Iran da Turkiya da wasu shugabannin kasashen tsakiyar Asiya suka halarta.

Jakadan Afghanistan a Pakistan, Hazrat Omer Zahkilwal da ya wakilci gwamnatinsa a wurin taron ya ce akwai bukatar raba harkokin tattalin arziki da na siyasa domin raya ayyukan kungiyar kasashen ta ECO da zimmar ganin an raya tattalin arzikin yankin.