AFCON: Najeriya Ta Tashi Kunnen Doki Da Equatorial Guinea

Dan wasan Najeriya, Victor Osimhen a karawar Najeriya da Equatorial Guinea

Dan wasan Equatorial Guinea Ivan Salvador ne ya fara zura kwallo a ragar Najeriya a minti na 36

‘Yan wasan Najeriya sun tashi kunnen doki a karawar da suka yi da Equatorial Guinea a gasar nahiyar Africa ta AFCON da ake yi a Ivory Coast a karo na 34.

An tashi a wasan da ci 1-1.

Wasan ya wakana ne a filin wasa na Abidjan, babban birnin kasar ta Ivory Coast.

Dan wasan Equatorial Guinea Ivan Salvador ne ya fara zura kwallo a ragar Najeriya a minti na 36.

Minti biyu bayan hakan dan wasan Najeriya Victor Osimhen ya farke kwallon.

Bangarorin biyu sun yi ta zubar damammaki a karawar, musamman ma ‘yan wasan Najeriya.

Najeriya za ta hadu da Ivory Coast a wasanta na biyu a wannan rukuni na ‘A’ a ranar 18 ga watan Janairu yayin da Equatorial Guinea kuma za ta fafata da Guinea-Bissau.

A ranar Asabar a wasan farkon bude gasar, Ivory Coast ta lallasa Guinea-Bissau da ci 2-0.