Lamuran sun abku lokacin da aka samu rahoton kwantar da mutane biyu a asibitin Valada mai zaman kansa a Yola da suka nuna alamu na kamuwa da cutar sankarau, lamarin da kwamishaniyar kiwon lafiya ta jihar Adamawa Dr. Fatima Atiku Abubakar ta ce a hukumance basu da kwararrun hujjojin barkewar cutar sankarau da zazzabin Lassa
Kwamishinar tace akwai wasu gwaje-gwaje da ake bukata kamin a tabbatar ko wadannan mutanen sun kamu da cutar sankarau. Kana ta bukaci jama’a su kwantar da hankulansu tare da ba da tabbacin ma’aikatarta tana cikin shirin ko ta kwana ko da an sami bullar sankarau.
A daya bangare kuwa rahoton da asibitin garin Song ya bayar na wasu majinyata, biyu daga cikinsu sun rasu. Ana kuma rade-radin sun kamu da cutar zazzabin Lasa ne bayan an ga alamun laulayin jikinsu yayi kama da cutar. Wannan ya haddasa zaman dardar.
Daga bisani bincike ya nuna ba cutar ba ce kamar yadda shugaban hukumar kula da lafiya matakin farko na jihar Adamawa Dr. Abdullahi Belel ya yiwa Muryar Amurka bayani.
Shugaban hukumar ya ba da tabbacin ba cutar ba ce bayan sakamakon binciken kwakwab da suka gudanar kan sanfirin jinin wadanda ake zaton sun kamu da cutar ya nuna ba su fama da ita. Dr, Belel ya ce hukumar ta budewa jami’anta dake sako-sakon jihar layin sakon kar-ta-kwana ta wayar selula don saukin ankara da ita da zaran sun ga alamun bullar cutar sankarau da ta zazzabin lasa.
Kokarin samun likitan asibitin Valada mai zaman kansa ya tabbatar ko mutanen nan biyu da ya yiwa jinya sun kamu da cutar sankarau ya cutura.
Rabon a sami bulluwar annobar sankarau a jihar Adamwa yau shekaru biyar inji hukkumomin kiwon lafiyar jihar.
Ga rahoton Sanusai Adamu da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5