Akalla mutane 7 ne suka rasa rayukansu sakamakon barkewar annobar kwalara a karamar hukumar Yola ta Arewa a jihar Adamawa.
Sanarwar da hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya (NEMA) ta wallafa a shafinta na X a yau Talata, tace jumlar mutane 71 ne aka kwantar a asibiti sakamakon annobar.
Hakan na zuwa ne bayan da hukumar yaki da yaduwar cututtuka da yin rigakafinsu ta Najeriya ta bayyana cewar, an samu mutane 1, 528 da suka kamu da cutar a jihohin kasar 31 da kananan hukumomi 107 kuma 53 daga cikinsu sun mutu.
A cewar NEMA, ambaliyar ruwan baya-bayan nan data gurbata hanyoyin samun ruwan shan al’umma ce ta janyo barkewar annobar.
Sanarwar ta kara da cewa ana cigaba da kula da sanya idanu akan wasu mutane su kimanin 100.
NEMA ta kuma kara bayyana cewar tana yin hadin gwiwa da gwamnatin jihar domin aiwatar da matakan gaggawa da zasu takaita tasirin annobar.