Limamin darikar Katolika Bishop Stephen Dami Mamza wanda ya biya tarar ya ce ceto fursinonin a ranar da ake tunawa da giciye Yesu Almasihu wanda ya bada ransa don ceton bil'Adama daga kangin zunubi, shine abinda ya kamata mabiya addinin Kirista su yi koyi da shi ga wadanda ke zaman kunci kamar yadda Littafi Mai Tsarki ke koyarwa.
Bishop Mamza ya kalubalanci fursinonin da aka yantar su baiwa marada kunya lokacin da suka koma garuruwansu wurin nuna halayya na gari. Ga wadanda ke zaman wa’adinsu kuwa, majamiyar ta mika masu kyautar kayan abinci da saniya na bukin Faska.
Daya daga cikin fursinonin da suka sami 'yancinsu Yakubu Bello ya yi nuni da raina sana’a da matasa ke nunawa a matsayin halayyar da ke jefa su aikata miyagun laifuffuka a hirar da Murya Amurka ta yi da shi tare da baiwa ‘yan uwansa shawarar kaucewa zaman kashe wando.
Da yake magana kan dangantakar jami’an da ke kula da gidajen yari da fursinoni, babban jami’i mai kula da gidan yarin Yola Malam Idi Ali Abubakar ya ce kamata ya yi jama’a su daina tsangwama da nunawa tsoffin fursinonin kyama wadanda a cewar sa suna iya zama mutane na gari.
Domin gudun kada fursinonin da aka yantar su shiga gararanba a cikin gari da zai sake sa su fadawa cikin miyagun hali, majamiyar Katolikan ta tanadi kudin mato ga wadanda ke nesa tare da yi masu alkawarin samar masu kudi na soma wata sana’a ga duk mai niyya.
Ga cikakken bayanin rahoton Sanusi Adamu.
Your browser doesn’t support HTML5