Adamawa: Ana Neman Yin Rufa-rufa Da Dukan Da Kakakin Majalisa Ya Yi Wa Dogarinsa

Dakin Majalisar Jihar Adamawa

Kimanin wata daya da kafofin yada labarai a Najeriya suka ba da labarin kakaki majalisar jihar Adamawa Kabiru Mijinyawa, ya yi wa sajen Umaru Dan sanda mai tsaron lafiyarsa duka, lamarin da rundunar yan sandan ta ce tana gudanar da bincike a kai.

Sai dai duk da cewar wannan batun ya shafi martabar majalisar, amma ya ‘kasa jan hankulan 'yan majalisar bisa rashin hujjar da ba a gabatarwa da majalisa ba kan korafin ba inji shugaban kwamitin ladabtarwa Hon, Musa Kallamu.

Da yake bayanin abin da ya wakana kakakin majalisar dokokin jihar Adamawa Hon. Kabiru Mijinyawa, ya karyata batun yana mai nuni da cewa gardama ce, inji shi sakanin jami'an tsaron gidansa shine ya fito don ya yi sulhunta amma aka yi masa gurguwar fahimta.

Muryar Amurka ta meni jin ta bakin mataimakin kakakin kuma shugaban kwamitin yada labarai na majalisar Hon. Sunday Peter, wanda ya ce majalisar ba ta karbi korafi kan wannan batu ba, kuma kakakin bai sanar da su ba duk da cewa a baya majalisar ce ke fitowa a duk lokacin da ba ta gamsu da wani rahoto ba.

Wani mai sharhi kan lamuram yau da kullum kuma lauya mai zaman kansa Barista, A. T. Shuhu, ya ce abin takaici ne kasancwar abu a bayyane kuma a ce ana neman a yi rufa-rufa yana mai zargin ‘yan jarida da hada baki.

Domin karin bayani saurari rahoton Sanusi Adamu.

Your browser doesn’t support HTML5

Adamawa: Ana Neman Yin Rufa-rufa Da Dukan Da Kakakin Majalisa Ya Yi Wa Dogarinsa - 3'22"