Adadin Wadanda Suka Mutu Sakamakon Cutar Coronavirus Ya Karu

Jimlar mutanen da suka mutu sakamakon cutar coronavirus a China ya zarta 900, yayin da cutar ke kara yaduwa a Birtaniya, lamarin da ya kai ga gwamnatin kasar ayyana cutar a matsayin gagarumar barazana ga lafiyar jama’a.

Jami’an kiwon lafiyar China sun ce an samu karin wasu mutane 97 da suka mutu a jiya Lahadi, abin da ya kai adadin mace-macen zuwa 908.

Yanzu kuma akwai wasu wadanda suka kamu da cutar da yawansu ya kai dubu uku da 62, lamarin dake nuna raguwar yaduwar cutar a kowacce rana kuma akwai kwarin gwiwar matakan da ake dauka suna tasiri.

Tuni dai barkewar wannan cutar ta shafi harkokin kasuwanci a kasar, kamar yadda Ministan Kasuwancin China Wang Bin ya bayyana.

Wang ya ce, “wasu wuraren sayar da kayayyaki, musamman na gona ba a samun komai, babu hatsi, babu man girki da sauran kayayyakin abinci irinsu taliya.”

A daya bangaren kuma, Birtaniya ta sanar da cewa mutune hudu sun kamu da cutar a yau Litinin, abin da ya sa adadin ya karu. Yanzu an tabbatar da mutanen da suka kamu da cutar sun kai takwas.

Ministan kiwon lafiya kasar Matt Hancock da ya ayyana cutar a matasayin barazana ga lafiyar jama’a, ya ba gwamnati karin karfin ikon kebe mutane, a wani mataki na kare yaduwar cutar.