Hukumar da ke yaki da cututtuka masu yaduwa ta Najeriya NCDC ta sanar da cewa an kara samun sabbin alkaluman wadanda suka kamu da cutar COVID-19.
A sanarwar da ta fitar a daren ranar Litinin 18 ga watan Mayu, hukumar ta ce an samu sabbin kamu mutum 216.
74 daga cikinsu a jihar Legas, 33 a jihar Katsina, 19 a jihar Oyo, 17 a jihar Kano, 13 a jihar Edo, 10 a jihar Zamfara, takwas a jihar Ogun.
Sauran jihohin sun hada da Gombe inda aka samu mutum takwas, takwas a Borno, bakwai a Bauchi, bakwai a Kwara, hudu a birnin tarayya Abuja, uku a Kaduna, uku a Enugu, biyu kuma a Rivers.
Ya zuwa yanzu dai gaba dayan adadin wadanda suka kamu da cutar ta COVID-19 a Najeriya ya kai 6,175.
Sanarwar ta kuma ce an sallami mutum 1,644 daga asibiti, bayan haka mutum 191 suka mutu sakamakon cutar.