Adadin Wadanda Suka Kamu Da COVID-19 a Duniya Ya Doshi Miliyan 100

Kasar Belgium na fatan yanayin sanyi da ake shirin bankwana da shi da riga kafin cutar COVID-19 zasu taimaka wajen yaki da cutar wadda coronavirus ke janyowa.

Adadin masu kamuwa da cutar COVID -19 a fadin duniya na kusantar miliyan 100. Da safiyar yau Asabar Jami’ar Johns Hopkin ta sanar da cewa sama da mutane miliyan 98 suka kamu da cutar a duniya kuma an sami mace-mace sama da miliyan 2.

“A halin da ake ciki, har yanzu cutar na yaduwa, amma muma muna da abubuwa biyu da zasu taimaka: riga kafi da raguwar yanayin sanyi." Abinda Yves Van Laethema, mai magana da yawun ma’aikatar lafiyar Belgium ya fada kenan game da cutar COVID-19 a kasar.

Mr. Yves ya ce ya na fatan yanayin da za a shiga zai taimaka wajen rage yawan mutanen da ake kwantarwa asibiti a Belgium.

Mutane kusan 690,000 ne suka kamu da cutar COVID-19, wasu fiye da 20,000 kuma suka mutu a kasar Belgium.