Adadin Wadanda Su Ka Mutu Sanadiyyar Gocewar Tudun Shara a Kampala Ya Kai 24

Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni.

Har yanzu ba a tantance yawan gawarwakin mutanen da ke karkashin tarkacen shara a birnin Kampala na Uganda ba.

Adadin Wadanda Su Ka Mutu Sanadiyyar Gocewar Tudun Shara a Kampala Ya Kai 24

Adadin wadanda su ka mutu sanadiyyar gocewar wani tarin tarkacen shara a Kampala, babban birnin kasar Uganda ya kai 24 zuwa jiya Lahadi yayin da masu ayyukan ceto tare da kayan tono ke ta kokarin gano wadanda abin ya rutsa da su, a cewar hukumar birnin.

Akwai yara akalla hudu cikin mutanen da gocewar tarkacen sharar ta kashe ranar Jumma’a a jujin Kiteezi, a cewar ‘yan sanda ga manema labarai.

Ana kyautata zaton mamakon ruwa ne ya janyo rugujewar tudun dinbin sharar. Amma har yanzu ba a tabbatar da abin da ya faru ba, to amma hukumar birnin ta amsa cewa akwai gazawa wajen tsari game da kasancewar wannan jujin

Mai Magana da yawun kungiyar Red Cross ta Uganda, Irene Nakasiita, ta ce babu alamar za a iya sake samun Karin masu rai.

Ba a iya tantance ko mutane nawa ne aka kasa sanin makomarsu zuwa yanzu ba. Shi dai wannan juji na Kiteezi katafare ne kuma ya na wata unguwar matalauta ne ta kan tudu, inda daruruwan tireloli ke zuwa su jibga kayan shara kulluyaumin. Hukumar birnin ta yi ta tunanin yadda za ta rufe shi tun bayan da ta ayyana cikarsa tun shekarun da su ka gabata.

Haka zalika wuri ne da ya kasance mara mai shi a wannan birni mai mutane miliyan 3, inda mata da yara ke yawan zuwa don tsince tsincen kayan bola da zummar sayarwa. Wasu mutane ma har sun gina gidaje daura da wurin.

Shugaban Uganda, Yoweri Museveni, ya bayar da umurnin a yi bincike kan wannan bala’in, ya na mai tambaya ta kafar sada zumunta ta X, wadda ada ake kira Twitter, dalilin da mutane ke zama daura da wani tarin shara haka.