Adadin Wadanda Su Ka Mutu A Gocewar Kasar Uganda Ya Karu Zuwa 26

Mutane sun taru a inda aka sami gocewar kasa a Uganda

Jami’an gwamnatin Uganda sun ce adadin mutanen da su ka mutu sanadiyyar gocewar kasa a ranar Asabar, a wani babban juji da ke Kampala babban birnin kasar ya karu zuwa 26, baya ga mutane 36 da har yanzu ba a san inda su ke ba.

Magajin Gari, Erias Lukwago, ya yi gargadi cewa, “Ta yiwu akwai karin" gawarwaki da dama karkashin baraguzai a jujin na Kiteezi da ke Gundumar Wakiso na birnin, inda nan ne ake zuba tarkacen sharar da ake kwasowa daga cikin birnin.

Ruwan sama kamar da bakin kwarya, wanda aka yi ta yi a wasu sassan gabashin Afirka ne, ya haddasa gocewar lakar, wadda ta binne mutane, da gidaje da kuma dabbobi.

Wurin da kasa ta zabtare a Uganda

Shugaba Yoweri Museveni ya ba da izinin biyan iyalan wadanda abin ya shafa shilling na Uganda miliyan biyar, kwatankwacin dalar Amurka 1,300 ga kowane mutum da ya mutu, da kuma shilling miliyan 1 ($ 270) ga ko wanne mutum daga cikin wadanda su ka ji rauni.

Shugaban kasar ya tura dakaru na musamman na sojojin kasar zuwa wurin da zaftarewar kasa ta rufta domin su taimaka a kokarin gano wadanda kasar ta rufta kansu.

Wadansu suna kwasar tarkace a juyin da kasa ta zaftare

Museveni ya ce yana son sanin dalilin da ya sa aka bar mutane su zauna kusa da irin wannan wuri "mai hadari ."

Mazauna wurin sun ce sun shafe shekaru suna kokawa game da hadarin da ke tattare da wurin, amma sun ce jami'ai sun yi watsi da su kuma ba su yi wani abu ba don rage yanayin kuncin rayuwa da su ke ciki.

A hirar shi da Kamfanin Dillancin Labarai na Faransa dan fafutuka Abubaker Semuwemba Lwanyaga ya ce, "ya kamata su yarda cewa sun yi kuskure," Ya kamata gwamnati ta tada mutanen daga wurin lokacin da ta tsaida shawarar zata maida wurin juji, ta biya su diyya, ba su jira sai bala'i ya faru ba.

Ku Duba Wannan Ma Sama Da Mutum 670 Sun Mutu Sakamakon Zaftarewar Kasa A Papua New Guinea - MDD