Adadin Wadanda COVID-19 Ta Kama a Duniya Ya Haura Miliyan 10

WHO Director Gen Tedros

Adadin wadanda cutar COVID-19 ta kama a duk fadin duniya ya haura miliyan goma, yayin da kusan mutum dubu 500 suka mutu.

A jiya Lahadi Jami’ar Johns Hopkins da ke bin diddigin yaduwar cutar ta fitar da wannan sabuwar kiddidgar.

A ’yan kwanakin da suka gabata, shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya Tedros Adhanom Gheberyesus ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa adadin ya doshi miliyan goma, ya kuma ce “ya zama dole a ci gaba da daukar matakan dakile yaduwar wannan annoba.

Har ya zuwa yanzu, Amurka ce ja-gaba a yawan masu dauke da cutar a duniya inda take da mutum miliyan 2.5 yayin da wasu sama da dubu 125 suka riga mu gidan gaskiya a cewar jami’ar ta Johns Hopkins.

A karshen makon nan jihohi biyar ne suka ba da rahotannin karuwar barkewar cutar a Amurka inda Florida ta samu sabbin kamu mutum dubu 9,585 da suka harbu da cutar cikion sa’a 24.