Kamar yadda likitoci a babban asibitin Gwamnatin tarayya wato (FMC) ke cewa yanzu haka wasu mutum 4 sun mutu lamarin da yakai adadin mutanen da suka mutu a jihar zuwa 7.
An samu nasarar jiyar 6 daga cikin 19 da tun farko aka kawo asibitin.
Da yake tabbatar da wannan adadin, Dr Ilya Atta wanda shine shugaban sashen jinya na asibitin, yace 3 daga cikin wadanda cutar ta hallaka sunmutu ne a wani waje tun ma kafin a iso dasu asibitin.
‘’Yace 19 ne aka kawo muna kuma tuni akayi jinyar 6 daga cikin su kuma har an sallame su, yace hakika 3 daga cikin wadanda cutar ta kashe sun mutu ne a wani wuri domin ba mu muka yi jinyar sub a, kodai a gidajen ko kuma asibiti masu zaman kansu acan ne suka mutu kuma da aka kawo muna su mu dai mu mika su ne ga ‘yan uwansu suje su binne su’’
Har wayau cibiyar ta shirya wani lacca ga maaikatan asibitin game da matakan kayiya.
Ga Ibrahim AbdulAzeez da Karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5