Jami’in ba da kulawar gaggawa a hukumar, Dr Mike Ryan, ya ce adadin zai iya hauhawa idan kasashen duniya ba su rungumi wani tsari kan yadda za a dakile yaduwar cutar ta coronavirus ba.
Yanzu haka cutar ta yi sanadin mutuwar kusan mutum miliyan daya a duk fadin duniya sannan ta harbi mutum miliyan 32.5 a cewar alkaluman da jami’ar Johns Hopkins ta fitar.
Gargadin jami’in na hukumar Lafiya ta duniya WHO na zuwa ne, yayin da nahiyar turai ke ganin barkewar cutar a karo na biyu, lamarin da ya sa gwamnatoci a sassan nahiyar suka maido da matakan hana yaduwar cutar.
Firai Ministan kasar Netherland, Mark Rutte ya bayyana hauhawan adadin masu kamuwa da cutar a matsayin “babban abin damuwa, yayin da kasar take ba da rahoton samun sabbin masu kamuwa da ita, wadanda adadinsu ya kai 2,777 a rana guda.