Hukumar kasa da kasa da ke sa ido kan mutanen da suke kaura, ta ce sama da bakin haure 32,000 ne suka mutu ko kuma suka bata a duk fadin duniya a tsakanin shekarar 2014 zuwa bara.
Ta kara da cewa mafi aksarin mutanen da ke mutuwa a tekun Meditareniya ne, yayin da suke kokarin tsallakawa daga yankin arewacin Afirka zuwa nahiyar turai.
Hukumar wacce ke karkashin Majalisar Dinkin Duniya, ta ce wannan adadi da ta fitar, kiyasi ne kawai, domin bai nuna asalin girman matsalar ba, saboda da yawa daga cikin mace-macen da ake samu, ba a kai rahotonsu, sannan ba a gano inda gawarwakin suke.
Amma dai duk da haka, masu bincike sun ce, wannan kiyasi ya fito da irin mummunan hadarin da ke gaban daruruwan dubban bakin hauren da ke saka rayukansu cikin hadari, yayin da suke neman mafaka ko kuma rayuwa mai inganci.
Rahoton ya nuna cewa, kusan mutum 18,000 sun mutu ko kuma sun bata a tekun Meditareniya a tsakanin shekarun 2014 zuwa 2018, sannan kashi biyu cikin kaso ukun wannan adadi, ba a san inda suke ba.
“Duk da rikicin da ke faruwa a Yemen, mutane na ci gaba da yunkurin tsallaka teku daga yankin arewa maso gabashin Afirka, zuwa yankin Bahrul Maliya da na Gabar tekun Aden. Akalla mutum 125 suka rasa rayukansu yayin da suke kokarin tsallaka teku daga Yemen a bara, idan aka kwatanta da mutum 53 da suka mutu a shekarar 2017. Inji kakakin hukumar mai sa ido kan bakin hauren, Joel Millima.