Mutum 46 Suka Kamu Da Coronaavirus A Najeriya

Hukumar dakile yaduwar hana cututtuka ta kasa da ake kira NCDC, ta ce an samu karuwar mutanen dake dauke da cutar coronavirus da suka kai 27 a Najeriya, ciki kuwa har da birnin Ibadan mai cunkoson jama’a.

A wata sanarwa da hukumar ta NCDC ta fitar, ta ce an samu karin wasu mutane biyu dake dauke da cutar coronavirus a jihohin Legas da Osun, yanzu adadin ya kai 46 kenan, bayan mutane biyu da aka sallama daga asibiti mutum daya kuma ya rasu sanadiyar cutar.

Wasu gwamnonin Najeriya biyu sun killace kansu bayan mu'amullar da suka yi da masu dauke da cutar, cikin su har da gwamnan jihar Edo Godwin Obasake da gwamnan jihar Ekiti Dr. Kayode Fayemi dake zama shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya. Dukkan gwamnonin sun gana da gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed da kuma babban jami’ain fadar shugaban Najeriya Malam Abba Kyari da suma suka kamu da cutar ta coronavirus.

A jihar Niger, a yau laraba 25 ga watan Maris dokar hana yawo daga karfe 8 na safiya zuwa 8 na maraice da gwamnati ta saka ta fara aiki, domin hana bazuwar cutar, kamar yadda gwaman jihar Abubakar Sani Bello yayi bayani ga al’umar jihar.

Ita ma gwamnatin jihar Legas ta dauki matakan hana bazuwar cutar da
suka hada da takaita zirga-zirgar ababen hawa da kuma rufe wasu
kasuwanni, in banda na abinci da shagunan magunguna.

Ga karin bayani cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Mutum 46 Suka Kamu Da Coronaavirus A Najeriya