Adadin Masu Cutar Coronavirus a Najeriya Ya Haura 110

A yayin da adadin masu dauke da cutar coronavirus ya haura 110 a Najeriya shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin hana yawo da harkokin shige da fice a jihohin Legas, Ogun da kuma birnin Abuja.

Wani rahoto da cibiyar hana yaduwar cututtuka ta kasa ta NCDC ta fitar a baya-bayan nan ya nuna cewa, mutum 111 ne suka kamu da cutar ta coronavirus a Najeriya.

Akasarin sabbin alkaluman sun fito ne daga jihar Legas da birnin Abuja,
inda Legas ke da mutum 9, sai kuma 5 a Abuja, Abinda ya sa Legas ke
kan gaba da mutum 69, 21 kuma a Abuja.

A jawabinsa ga 'yan Najeriya game da wannan cuta ta coronavirus, shugaban Najeria Muhammadu Buhari yayi kira ga 'yan kasar da su kasance masu taka-tsan-tsan, kuma ya bada umurnin hana zirga zirga da shiga da fita jihohin Legas, Ogun da kuma birnin Abuja, har nan da makonni biyu, domin magance yaduwar annobar cutar coronavirus.

Wasu mazauna birnin Legas sun nuna amincewarsu da wannan mataki, sai dai sun ce akwai matsala ga talakawa dake fita domin neman abinda zasu ci.

Alhaji Ado Dan Sudu, wani shugaban al'ummar 'yan arewacin Najeriya a birnin Legas, ya fadi cewa idan cutar coronavirus bata kashe talaka ba, lallai yunwa zata kashe shi a gida sakamakon dokar hana fita da aka sanya.

Gakarin bayani cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Adadin Masu Cutar Coronavirus a Najeriya Ya Haura 110