Yawan masu dauke da cutar coronavirus a duniya ya haura 2.7 a cewar Jami’ar Johns Hopkins.
Jami’ar ta bayyana hakan ne a shafinta na yanar gizo inda ta ce adadin ya ka miliyan 2,790,986.
Amurka ce kasar da ta fi yawan masu cutar a Duniya inda take da mutum 890,524.
Sai Spaniya mai mutum 219,764 yayin da Italiya ke biye da ita da mutum 192, 994.
Ita dai Faransa tana da mutum 159,495 sannan Jamus na da mutum 154,545 yayin da Burtaniya ke da mutum 144,635 da suka kamu da cutar.
Hakan na faruwa ne yayin da adadin mutanen da suka mutu sanadiyyar cutar ta coronavirus a Amurka ya haura 50,0000, a cewar Jami’ar ta Johns Hopkins.
Ya zuwa ranar 24 ga watan Afrilu, adadin mace-macen ya tsaya akan mutum 51,017 a cewar Jami’ar.
Birnin New York ne ya kasance matattarar cutar inda mutum 16,646 suka rasa rayukansu a cewar shafin yanar gizon Jami’ar.
Akalla mutum 96,677 suka warke daga cutar ta COVID-19 a Amurkan.