Hakan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da ‘yan Najeriyar ke mayar da martani akan wani rahoto da bakin duniya dake cewa, ‘yan kasar miliyan 7 ne zasu fada komar talauci a bana sanadiyyar tashin farashin kayayyaki.
A farkon wannan shekara ta 2022 ne, bankin na duniya yayi hasashen cewa, jimlar ‘yan Najeriya miliyan 6 ne zasu fada cikin komadar taulauci zuwa karshen shekarar.
Amma wani rahoto da bankin ya fitar a baya bayan nan, ya ce adadin zai karu da miliyan guda, sakamakon yadda farashin kayayyakin abinci da sauran kayan amfanin yau da kullum ke tashin gwauron zabbi a kasar.
Da-ma dai Hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya shine mafi sauri a duniya gabanin barkewar yaki tsakanin Rasha da Ukraine kuma yakin ya kara ta’azara farashin kaya da ayyukan yau da kullum a kasar, in ji rahoto.
Wasu ‘yan Najeriya da suka tofa albarkacin bakin su dangane da wannan rahoto na bakin duniya sun ce tsaban talauci har ya sa sun rasa matansu, yayin da wasu kuma suka ce kudin da su ke samu, ba ya isan su kudin cefanen gida.
A hirar shi da Muryar Amurka Malam Zakari Ya’u Aliyu, wani masi sana’ar siyar da nama a Kano ya ce baya ga talakawa dake rayuwa a yanayi na hannu baka hannu kwarya, hauhawar farashin kayayyakin na mummunan tasiri akan ‘yan kasuwa masu kananan jari da sana’o’in hannu a kasar.
A nata bangaren, kungiyar masu masana’antu ta Najeriya MAN, ta bakin Alhaji Sani Hussaini, shugaban kungiyar a shiyyar Kano da Jigawa tace yanzu haka ‘yayan ta na dandana kudar su, sanadiyyar wannan yanayi na tashin gwauron zabi na farashain kayayyaki da ‘yan kasar fuskanta.
Faduwar darajar Naira, da rashin wutar lantarki da tsadar man gas na daga cikin dalilan da bankin na duniya ya ambata sune sanadin tashin farashin da ake gani wadda ya haifar da sabon talaucin ga ‘yan Najeriya miliyan 7.
Bakin na duniya yayi dai-dai da na kungiyar masu masana’antun ta Najeriya akan haka da kuma matakan da mahukuntan kasar ya kamata su dauka.
Tuni hukumomin na Najeriya ke cewa, suna iya kokari domin ganin al’amura sun dai-daita a kasar.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5