Abuja: Za'a Mayar Da 'Yan Gudun Hijra Borno

'Yan gudun hijira

Wasu 'yan gudun hijira dake Abuja babban birnin Najeriya sun nemi a mayar dasu jihar Borno, jiharsu ta asali.

Daraktan hukumar bada agajin gaggawa na yankin Abuja Alhaji Abbas Idris ya zanta da Muryar Amurka akan irin tsarin da hukumar zata bi na mayarda 'yan gudun hijiran zuwa Maiduguri jihar Borno..

Alhaji Abbas yace akwai wadanda su da kansu suka nuna sha'awar komawa jiharsu. Sun bi hanyoyin da zasu bi su mayar dasu cikin kwanciyar hankali wannan ko ya hada da zuwansu Maiduguri su gani da idanunsu yanayin garin. Sun yi magana da gwamnatin jihar da kuma hukumar bada agaji ta jihar Borno.

Ba duka 'yan gudun hijiran za'a mayar Maiduguri ba. Wadanda suka nema su ne za'a mayar dasu. Mai wurin da suke zama yanzu a Abuja ya sayarda jigajen saboda haka dole su bar wurin.

A Abuja akwai sansanin 'yan gudun hijira wajem wurare bakwai. Rikicin Boko Haram ya korosu zuwa Abuja.

Saidai wurin da aka nuna masu a Maiduguri sun ce bai yi masu ba saboda babu dakin kwana. Rumfar leda mutane ke kwana ciki kuma su musanta batun cewa su ne suka nema a mayar dasu Maiduguri.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

'Abuja: Za'a Mayar Da 'Yan Gudun Hijra Borno - 2' 54"