Mataimakiyar babbar jami'ar diflomasiya a ofishin jakadancin Amurka dake Abuja Maria Brewa tace shirin musayar dalibai an kirkiroshi ne domin cike gibin fahimtar al'umma da al'adun Amurkawa.
Tace irin ziyarar da Amurkawa ke daukan nauyi domin samun horo baya tsayawa a manyan birane kawai ,a'a dalibai na samun damar zagayawa zuwa karkarar Amurka.
Daliban da suka anfana da shirin sun hada da gwamnan Legas na yanzu Ambode da gwamnan Edo Oshiomole da Farfasa Attahiru Jega tsohon shugaban hukumar zaben Najeriya. Sauran sun hada da Alhaji Yusuf Maitama Sule da mataimakin shugaban Najeriya na farko Dr Alex Ekweme.
Kimanin 'yan Najeriya dubu biyar ne suka anfana da shirin tun lokacin da aka farashi zuwa yanzu.
Darakta a hukumar dake kula da jami'o'in Najeriya Mr. Chris Maiyaki yace akwai darussa iri-iri da mutum zai koya a Amurka. Akwai wata baturiyar Amurka da tayi fira da harshen Hausa a taron.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5