Abubuwan Da Suka Wakana a Taron NEC Na APC

Shugaba Buhari

Kwamitin gudanarwa na kasa na jam'iyyar ya nada gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni a matsayin shugaban kwamitin riko na APC.

An dauki wannan matakin ne a taron shugabbani na APC da aka gudanar yau, bayan da aka soke kwamitin zartarwa na jam'iyyar.

Mai baiwa shugaban Najeriya shawara kan harkokin da suka shafi harkokin sada zumunta, Bashir Ahmad ne ya bayyana hakan a kan shafinsa na Twitter.

A cewarsa an soke kwamitin zartarwa na APC ne "biyo bayan shawarwarin da shugaba Buhari ya bayar."

Taron wanda aka gudanar a fadar shugaban kasar Najeriya da ke Abuja, ya samu halartar gwamnonin jihohin Jigawa da Filato da Yobe da Ogun da Legas da Kebbi da Kano da kuma Kaduna.

Taron NEC

A cikin makon da ya gabata ne jam'iyyar ta APC ta shiga wani rikici wanda ya fara bayan da aka dakatar da Adams Oshiomhole a matsayin shugaban jam'iyyar.

Adams Oshiomohle

Jim kadan bayan nan, kwamitin zartarwa na APC ya nada Sanata Abiola Ajimobi a matsayin shugaba na rikon kwarya na jam'iyyar.

A jiya laraba ne dai shugaba Muhammadu Buhari ya ayyana Victor Giadom a matsayın shugaba na rikon kwarya.