Abubakar Yellow: Zamu Dawo Da Martaba Wikki Tourist Fc

Abbakar Yellow

Babban mai bada shawara a kungiyar kwallon kafa ta Wikki Tourist Fc dake jihar Bauchi a tarayyar Najeriya, Mal Abbakar Abbakar Yellow, (Chief Consultant Wikki) ya bada tabbacin yin wasu sauye-sauye a kungiyar domin fuskantar kakar wasannin shekarar 2018.

Abbakar Yellow, ya ce a matsayinsu na Sabin shuwagabanni a kungiyar zasu duba duk abinda ya dace domin dawo da Martabar kungiyar musamman bangarorin da suka shafi ‘yan wasa inda zasu duba wasu ‘yan wasan da basu da amfani a kungiyar domin shigo da matasa masu amfani.

Haka kuma zasu dubu bangaren fasaha (Technical Crew) na kungiyar da kuma bangaren walwala da jin dadi (Welfare) domin yin abinda ya kamata.

Ku Duba Wannan Ma Sani Katu Ya Musanta Zargin NFF Hana Wasu Shiga Takara

Kungiyar Wikki tana fama da rashin filin wasa a sakamakon gyara da ake yi a filin wasanta na Abubakar Tafawa Balewa, dake Bauchi inda a kakar wasan da ta gabata 2017/18 ta buga dukkannin wasaninta a jihar Plateau, sai dai Abbakar Yellow yayi kokari wajan dawo da kungiyar da buga wasanta a jihar Gombe, domin ya fi cancanta a gareta maimakon Plateau.

Abbakar Yellow, ya ce yana kyautata zaton cewar gwamnatin Jihar Bauchi a karkashin jagorancin Gwamna Moh'd Abdullahi Abubakar zata kammala gyaran filin wasan kafin kakar wasa ta 2018/19.

Yayin hirar sa da wakilin dandalinvoa a jihar Bauchi, ya ce kungiyar karkashin jagorancin Sababin shuwagabannin zata kirkiro da wata gasar kwallon kafa ta matasa dake cikin garin Bauchi, domin sanya ido wajan zakulo matasa masu hazaka wadanda za a iya shigo dasu cikin kungiyar ta hanyar sanya Technical Crew, wajan zabo yaran wadanda zasu iya taimakawa kulob din

Bayan haka ya yaba wa Al'ummar jihar Bauchi da kuma kungiyar magoya bayan Wikki Tourist bisa irin kokarin da suke yi wajan ganin kulob din ya ci gaba.

Your browser doesn’t support HTML5

Abbakar Yellow: Zamu Dawo Da Martaba Wikki Tourist Fc