Abubakar Shekau: “Ruwa Ya Karewa Dan Kada” – inji Kanal Usman Kuka Sheka

Abubakar Shekau

Abubakar Shekau

Rundunar sojojin Najeriya tace sabon fefan bidiyon dake nuna shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau, magana ce wadda bata da tasiri kuma farfaganda ce kawai.

A wata tattaunawa da wakilin Muryar Amurka Nasiru Adamu El-Hikaya, yayi da Daraktan yada labarai na rundunar Sojin Najeriya Kanal Usman Kuka sheka, yace wannan wata alamace da ke nuna cewa Ruwa ya ‘karewa ‘dan Kada, kuma ikirarin da Shekau yake na cewa yana cikin musulunci yana kuma ayyuka don musulunci, wannan ya tabbatar da cewa shi ba musulmi bane.

Ya ci gaba da cewa meyasa Shekau in musulmi ne bai fito sallar Idi ba? ya kuma ce suna da tabbacin cewa a cikinsu ma ba a barinsa yana jan Sallah. Kuka Sheka, yace duk wasu abubuwa da Shekau yace cikin bidiyonsa, a gani a ‘kasa shine, domin kowa ya sani cewar anfi karfin ‘yan ta’addan Boko Haram, lokaci ne kawai ya rage.

Rundunar sojan Najeriya dai tace tana nazari mai zurfi akan sabon hotan bidiyon, kuma ta yi imanin cewa ba a dade da daukar hotan ba, sabanin hotan bidiyon da kungiyar Boko Haram ta fitar na baya wanda ‘yan kungiyar ke ikirarin sunyi sallar Idi, ita kuma rundunar sojan Najeriya tace tsohon bidiyo ne.

Kuka Sheka dai yace wannan wani sabon salo ne na Shekau, domin ya nuna cewa yana da tasiri wanda kuma bashi da shi, saboda a zahiri abin da suke kokarin bayyanawa ba haka yake ba a ‘kasa.

Saurari tattaunawar Nasiru Adamu El-Hikaya da Daraktan yada labarai na rundunar Sojin Najeriya Kanal Usman Kuka sheka.

Your browser doesn’t support HTML5

Abubakar Shekau: “Ruwa Ya Karewa Dan Kada” – inji Kanal Usman Kuka Sheka - 2'20"