Shugaban wata kungiya da ake kiranta da One Nigeria wato (Najeriya Daya ce) ya bukaci yan’kasar da su kara hakuri tare da yi ma gwamnati uzuri a yakin da ta ke yi kan matsalar ta tsaro
Wadannan bukatu na shugaban kungiyar Muhammad Saleh Hassan na zuwa ne a daidai lokacin da wasu 'yan Najeriya daga yankin arewacin kasar suka dauki matakin gudanar da zanga zanga da bayyana korafe korafensu ta yanar gizo don jawo hankalin gwamnati ga mawuyacin halin da yankin arewa ke ciki,
Amma ga wasu yan Najeriyar wannan maganan ba haka take ba, ana su suna ga ta hanya zanga zanga da kiraye kiraye ta yanar gizo kadai ya ragewa talaka ya yi da gwamnati zata ji kukansa ta kuma san halin da ya ke ciki, kamar yadda shugaban kungiyar matasa ta Arewa maso gabas Alhaji Abdulrahaman Buba Kwacham ya bayyana
A cigaba da wannan fafutuka wasu sai da ta kai su ga bude shafuka a yanar gizo na musamman don fadakar da yan’kasa akan abubuwan da ke faruwa na tsanartar yanayi da tabarbarewar lamura da kuma nuni kan yanda za su dau mataki, Ita ma Fittaciyar yar’ gwagwarmaya Aisha Yesufu ta na jagorantar wani gaggami a yanar gizo wanda ya baiwa yan' kasar damar fitowa su bayyana korafe korafensu
A na su bangaren kungiyar marubuta na arewa a yanar gizo karkashin jagorancin Kwamrad Abba Sani Pantami takardar ƙorafi suka turawa hukumomin tsaron kasar kan matsalar
Daya daga cikin ginshikan damokradiyya dai shine fadin albarkacin baki ba tare da fuskantar wata barazana ba yanzu zu abin jira agani shine irin tasirin da irin wadannan kiraye-kiraye zasuyi wanjen fargar da gwamnati abubuwan dake damun jamarta
Saurari Rahoto cikin sautin Shamsiyya Hamza Ibrahim daga Abuja Najeriya.
Your browser doesn’t support HTML5