Zanga-zangar mutanen Najeriyar na kira ne da a kauracewa dukkan wasu kamfanonin Afrika ta Kudu da suke a Najeriya kamar su MTN, DSTV, SHOPRITE da makamantansu.
Suna ganin yin hakan ne kadai zai iya shafar tattalin arzikin can kasar saboda irin tasirin karauwar da suke yi da ‘yan Najeriya kullum safe ta maganar harkokin sadarwa.
Sai dai wani mai fashin bakin al’amura Dakta Nasir Kurfi yace ‘yan Najeriya ba su da mafita ko makwafin hanyoyin sadarwar da zai iya sawa har su kauracewa na Afrika ta Kudu.
Yace da muna da kamar kamfanonin sadarwar da zasu iya mana abinda muke samu daga na Afrika ta Kudun to da abin zai yi matukar tasiri kuma zai taba tattalin arzikinsu musamman nan gaba.
Game da maganar barazanar MTN na cewa in suka rufe ofishinsu na Najeriya mutane zasu rasa guraben ayyuka, sai yace MTN ba zasu iya rufe kamfaninsu ba don sun kafu ne da kudin da suka samu a Najeriya.
Daga karshe ya nuna cewa ga dukkan alamu gwamnatin Afrika ta Kudu ta damu kasancewar kama mutane sama da 300 a kasar za kuma a kai su kotu game da wannan matsala.
Your browser doesn’t support HTML5