Abin Sani Kan Rigakafin Yara

Wani yaro ana yi mashi allurar rigakafi

Rigakafi wani tsari ne wada ake amfani da shi domin kare mai lafiya daga kamuwa da cuta. Akan fara tun daga ranar da aka haifi yaro. Ya kamata bayan wankan haihuwa da sauran su, a ba yaro dukan alurai da ya kamata, kamar aluran ciwon shan inna da sauransu.

In har an bari ya makara ba a yiwa jariri alluran da ya kamata ba, kar ya kai sati ba a bada wadanan rigakafi ba.

Ya kamata a bama dan jariri rigakafi yada ya kamata saboda jikin yaro yana da rauni akan ainihin garkuwan jikinsa. A wanan lokacin ne ya kamata a fara yi mashi rigakafi hawa hawa har lokacin da yaron zai kai wata tara.

A wanan lokaci, rigakafin da za'a bayar sun hada da na tarin fuka, ciwon shan inna, ciwon hanta (hepatitis), kyanda, bakon dauro, da sauransu.

Ya kamata kafin jariri ya kai wata tara za a tabatar an bada duk wadanan aluran rigakafin.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Abin Sani Kan Rigakafin Yara - 1:32