Abin Da 'Yan Najeriya Ke Cewa Kan Harin Da Aka Kai Kan Jirgin Kasa

Your browser doesn’t support HTML5

A makon da ya gabata ne ‘yan bindiga suka kai hari da bom a hanyar jirgin kasa tsakanin Abuja da Kaduna a arewacin Najeriya.
A makon da ya gabata ne ‘yan bindiga suka kai hari da bom a hanyar jirgin kasa tsakanin Abuja da Kaduna a arewacin Najeriya. Lamarin dai ya tilasta dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa a kan hanyar na kusan kwana guda, abin da ya janyo asara mai yawa. Aisha Mu’azu ta jiyo ra’ayoyin wasu ‘yan Najeriya masu amfani da jirgin kasa a game da matakin da ya kamata gwamnati ta dauka don kaucewa matsalar a gaba.