A Wata hira da aka yi aka yi da shi, Gwamnan Zamfara Dauda Lawal ya zargi Karamin Ministan tsaro, Bello Mutawalle na da hannu akan matsalar ‘yan bindigar da ta addabi jihar, inda ya yi kira ga Ministan da ya ajiye mukaminsa don ya wanke kansa.
Ba da jimawa ba bayan furucin gwamna Dauda, shi ma Mutawalle ya mai da martani inda ya wanke kanshi akan wannan zargin yana mai cewa:
“Sam ba shi da alaka da kalubalen tsaron ‘yan bindigar da ta addabi jihar ta Zamfara, asali ma kokari ya yi na ganin an bi hanyoyin da doka ta tanada domin ganin an samu kwanciyar hankali da sake dawo da tsaro a jihar ta Zamfara.
Ministan har ma ya yi rantsuwa da Qur’ani don barranta kansa da wannan zargi.
Sannan ya kalubalanci gwamnan Dauda da mukarrabansa da su ma su yi irin wannan rantsuwar, matukar dai ba su da hannu a cikin kalubalen tsaron.
Wannan sa-in-sa a tsakanin shugabannin al’umar ta zama abin da jama'ar jihar suka fi tofa albarkacin bakin su akai.
"Abin da nake so na ce ce-ce-ku-cen da ke faruwa tsakanin gwamna Lawal da tsohon gwamna Mutawalle, ba shi muke bukata ba yanzu, muna neman hadin kansu ne domin ci gaban jihar Zamfara. In ji Abba Mayana.
A saurari rahoton AbdulRazak Bello Kaura:
Your browser doesn’t support HTML5