Babbar 'yar takara cikin matan da ke neman mukamin shugaba kasa a Najeriya ta janye daga takarar da take yi.
'Yar takarar ta ce matakin yunkuri ne na taimakawa wajen hada hancin sauran jam’iyyun don yin adawa da manyan jam'iyyu biyu na kasar wato APC mai mulki da kuma PDP da ta kasnace babbar jam'iyyar adawa.
Oby Ezekwesili ta sanar da cewa za ta janye a matsayin ‘yan takara ta Jam'iyyar Allied Congress Party of Najeriya ko kuma ACPN a takaice, a cikin wasu sakkonin da ta saka a shafinta na twitter a yau Alhamis.
Ita dai Ezekwesili, wacce tsohuwar minista ce a Nigeria kuma tsohuwar shugabar bankin duniya, ta ce ana bukatar maye gurbin Shugaba Muhammadu Buhari na APC da kuma babban jam'iyyar adawa.
Ezekwesili ta na cikin daya daga cikin 'yan takara 73 da ke takara a zaben shugaban kasar da za’a yi a Nigeria a ranar 16 ga watan Fabrairu mai zuwa, amma da yawa suna ganin zaben takara ce kawai a tsakanin shugaba Buhari na APC da Atiku Abubakar na jam’iyyar adawa ta PDP.