Abin Da Wasu ‘Yan Najeriya Ke Cewa Kan Kutsen WhatsApp

FILE - The WhatsApp app logo is seen on a smartphone in this picture illustration.

Mutane da dama a sassan duniya, na nuna kaduwarsu da bayanai da suka nuna cewa, an yi kutse a manhajar WhatsApp.

A yau kamfanin Facebook, wanda shi ya mallaki manhajar, ya yi kira ga masu amfani da ita da su sabunta manhajar da wata sabuwa da ya samar wacce ta toshe kafar kutsen da aka samu.

Wani kamfanin Isra’ila mai suna NSO ne ya samar da manhajar da aka yi kutsen da ita, amma ya ce shi ya kerawa wasu hukumomin gwamnati ne, domin shi kansa bai taba amfani da ita ba.

WhatsApp dai bai fadi iya adadin mutanen da kutsen ya shafa ba.

‘Yan Najeriya ma ba a bar su a baya ba, wajen bayyana ra’ayinsu kan wannan kutse.

“Mu tunaninmu, duk labarin da mutum zai saka, ya rika yin taka tsantsan kan labarin da zai saka, ya rika sanin abin da zai rubuta.” Inji Malam Musa, wani mai amfani da manhajar.

Malam Ado Dan Sudu na kungiyar ci gaban ‘yan Arewa Legas ya ce, “wannan lokaci da aka samu ilimin kerekeren zamani a duniya (technology) abin ci gaba ne, abin kuma ci baya ne.”

Ya kara da cewa, “takaicin da yake cikinsa shi ne, irin kutsen da ake yi ta hanyar internet ga bankuna da ainihin asusun ajiyar kudi na mutane.”

Wata kididdiga da wata kungiya mai suna “We are Social” ta yi a Najeriya, ta nuna cewa, akalla kashi 41 na ‘yan kasar cikin 100 ne ke amfani da kafar ta WhatsApp.

Saurari cikakken rahoton Babangida Jibril daga Legas:

Your browser doesn’t support HTML5

Abin Da Wasu ‘Yan Najeriya Ke Cewa Kan Kutsen WhatsApp - 3'53