Abin Da Masana Siyasa, Shari’a Ke Cewa Kan Dage Zaben Najeriya

Wani dan sanda na gadin kayayyakin zabe a a Yola jihar Adamawa 15, Fabrairu 2019

Bayan shafe wuni a na ta raderadin yiwuwar dage babban zaben Najeriya a yau Asabar din nan, shugaban hukumar ya bayyana dage zaben zuwa 23 ga watan nan na Fabrairu

Shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu, ya kara da cewa shi ma zaben gwamnonin an dage shi daga 2 ga watan gobe zuwa 9 ga watan na Maris.

Dage zabe a Najeriya ba sabon abu ba ne don hakan ya faru a 2015 da hakan ya haddasa caccaka daga ‘yan adawa a lokacin wato jam’iyyar APC da ke kan karaga yanzu.

Masana da dama sun yi ta sukar wannan mataki kan yadda aka dage zaben a kurarren lokaci, suna masu cewa matakin zai haddasa shakku a zukatan ‘yan Najeriya.

Ko da yake, masana a fannin shari’a, sun ce matakin na INEC bai take doka ba, domin kundin tsarin mulkin kasar ya ba ta damar ta dauki duk matakin da ya dace domin ganin an yi zabe karbabbe.

Saurari fashin bakin Dr. Usman Bugaje, mai sharhi kan harkokin siyasa a Najeriya:

Your browser doesn’t support HTML5

Abin Da Masana Siyasa, Shari’a Ke Cewa Kan Dage Zaben Najeriya - 5'26"