Abin Da Kungiyoyin Kare Hakkin Bil’adama, Lauyoyi Ke Cewa Kan Hukuncin Da Kotu Ta Yankewa Mubarak Bala

Mutum mutumin da ke kofar wajen kotun tarayya da ke Abuja, Najeriya, Satumba 11, 2019.

Kasa da sa’o’I 24 da bayyana hukuncin babbar kotun Kano na shekaru 24 a gida gyaran hali akan Mubarak Bala, wani Matashi da kotun ta samu da laifin yin sabo ga addinin musulunci da kuma yunkurin tunzura Jama’a, kungiyoyin kare hakkin bil’adama da lauyoyi sun fara bayyana ra’ayi

Yayin da al’umar gari keyin maraba da hukuncin kotun.

A shekara ta 2020 ne, Matashi Mubarak Bala ya wallafa wani rubutu a shafin sadarwa na facebook mai kunshe da laffuzan sabo ga addinin musulinci da Annabi Muhammadu.

Tun a wancan lokaci ne Jami’ai suka kama shi a gidan sa dake Kaduna daga bisa suka gurfanar da shi a gaban kuliya akan baman batutuwa guda biyu wato batanci ga Annabi Muhammadu da kuma yunkurin tunzura jama’a, wadanda suka kunshi tuhume-tuhume guda 18.

A zaman kotun na jiya karkashin jagorancin, mai shari’a Faruk Lawan, Mubarak Bala ya tabbatarwa da kotun cewa, babu ko shakka ya aikata dukkanin tuhume-tuhumen 18, kuma sabanin abin da lauyansa ke kokarin fadawa kotu shi-fa kwakwalwar lafiyarta kalau.

Ku Duba Wannan Ma Fadar Shugaba Buhari Na Da Hannu A Kin Rantsar Da Ni-Garba Chede

Daga nan ne, alkalin ya yanke masa hukuncin shekaru 45 bisa irin na lissafin kotu.

Wasu daga cikin al’umar gari sun bayyana ra’ayin su dangane da wancan hukunci na babbar kotun Kano inda suke cewa hukunci ya yi daidai domin zai dakile irin wadannnan munanan maganganu da ke haddasa fitina cikin al'umma.

Comrade Haruna Ayagi, shi ne Daraktan kungiyar human rights network of Nigeria, masu kare hakkin bil’adama. Ya ce abun da suke bibiya shine a yi maka hukunci, ba tare da cewa a zalunce ka ba.

Kwararru a fagen shari’a sunce Mubarak Bala nada ‘yanci daukaka kara akan wannan hukunci.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyoyin Kare Hakkin Bil’adama Da Lauyoyi Sun Fara Bayyana Ra’ayi Game Da Hukuncin Kotu Kan Mubarak Bala