Abin Da Ke Tafe: Hira Ta Musamman Da Muryar Amurka Ta Yi Da Buhari, Atiku

Shugaban Najeriya mai ci Muhammadu Buhari da dan takarar jam'iyyar adawa ta PDP Atiku Abubakar, wadanda za su fafata a neman kujarer shugaban kasa

Sashen Hausa na Muryar Amurka ya yi tattaki har zuwa Najeriya inda Aliyu Mustapha Sokoto ya yi hira da shugaba mai ci Muhammadu Buhari da dan takarar jam’iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar kan zaben 2019 da ke tafe.

A Najeriya, makwanni kadan ne suka rage a tunkari zaben gama-gari na 2019, inda 'yan takarar da suka fito daga jam'iyyun siyasa sama da 90, za su nemi kujeru daban- daban.

A dai ranar 16 ga watan Fabrairu za a gudanar da zaben shugaban kasa da na majalisar dokokin kasar.

A wannan zabe, jami'yya mai mulki ta APC da babbar jam'iyyar adawa ta PDP, sune hankula ya fi karkata a kansu, watakila, sanadiyar dadaddiyar hamayya da ke tsakaninsu.

Dangane da haka, Sashen Hausa na Muryar Amurka ya yi tattaki har zuwa Najeriya inda Aliyu Mustapha Sokoto ya yi hirarraki na musamman da shugaba mai ci Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC, da dan takarar jam’iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar.

Aliyu Mustapha Sokoto (Hagu) da Shugaba Muhammadu Buhari (Dama) yayin tattaunawar

Shin kan wadanne batutuwa suka tattauna, a wannan hira ta musamman da Muryar Amurka ta yi da ‘yan takarar?

Dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar (Hagu) a hirarsa da Aliyu Mustapha Sokoto (Dama)

Ku biyo mu a shirye-shiryenmu na gaba a rediyo da talabijin domin sauraro da kallon wadannan hirarraki na musamman da 'yan takarar.