Yau kwana guda kenan, bayan da hukumar zaben Najeriya ta INEC ta dage babban zaben kasar da aka tsara za a yi a ranar Asabar din da ta gabata.
Da ba a dage zaben ba, da yanzu an fara tattaro sakamakon zabe daga sassan kasar.
Amma hukumar INEC ta dage zaben bayan da ta ce an samu tangarda wajen shirye-shriyen da take yi, lamarin da ya sa aka rika sukar matakin da hukumar ta dauka.
Shi ma Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, wanda ke neman wa'adi na biyu, ya nuna takaicinsa, kan dage wannan zabe, wanda za a yi ranar 23 ga watan Fabrairu.
Shugaban ya fadi cewa bai ji dadin wannan matakin ba, ganin cewa duk kudaden da hukumar ta bukata an ba ta, kuma ‘yan Najeriya da ‘yan siyasa sun yi shiri mai kyau domin shiga wannan zaben.
A cewar shi, dage zaben zai iya kawo larurori daban daban ga mafi yawan ‘yan Najeriya musamman wadanda suka yi tafiye-tafiye domin su je jihohin da suka yi rijista domin su kada kuri’arsu.
Shugaba Muhammadu Buhari ya ce gwamnatin sa za ta sa ido, sannan za ta tattauna da hukumar zaben kasar, domin duba hanyoyin da za’a kawar da aukuwar irin wannan larurar da ta ce ta fuskanta, abin da ya tilasta aka daga wannan zabe.
'Yan Najeriya da dama sun kwanta a ranar Juma'a da niyyar za su wayi gari domin hallara zuwa rumfunan zabe, amma sai suka samu labarin dage zaben.
Saurari cikakken rahoton Umar Faruk Musa daga Abuja:
Your browser doesn’t support HTML5