Dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya kaddamar da yakin neman zabensa a jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya.
Rahotanni sun ce daruruwan magoya bayan jam’iyyar ta PDP ne suka hallara a filin taron da aka kaddamar da yakin neman zaben na PDP.
“An ce mana mu jam’iyyar PDP ba mu da magoya baya a arewa maso yamma, wadannan ba jama’a ba ne.? In ji Atilku
Ya kara da cewa, “abin da ke gabanmu shi ne, zabe tsakanin kawar da talauci da rashin zaman lafiya da rashin aikin yi.”
Daga cikin gaggan jam’iyyar ta PDP da suka halarci taro, akwai tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal da tsohon gwamna Attahiru Bafarawa.
Atiku zai yi tarkara ne da shugaba mai ci Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC, a zaben da za a yi ranar 16 ga watan Fabrairun badi, duk da cewa akwai wasu 'yan takara a sauran jam'iyyun kasar.
Tun kusan makwanni biyu Buhari ya kaddamar da na sa yakin neman zaben.
Saurari rahoton Murtala Faruk Sanyinna domin jin jawabin Atiku:
Your browser doesn’t support HTML5