Aamir khan Ya Kafa Tarihi A Kasar China

Aamir khan ya kafa tarihi a China, da fim dinsa mai suna Dangal,

Fim din ya taka rawar gani a China, koda yake babu wanda yayi harsashen cewa fim din Indiya zai yi irin wannan abun mamakin a kasar China,

Kasar ta China bada dadewa ba ta fara karbar karin fina finan Indiya, a cikin irin wadannan fina finan Dangal, na fitatcen jarumin nan Aamir Khan, ne ya samu karbuwa a kasar China fiye da kowane fim daga Indiya.

Tarihin da fim din ya kafa sune kamar haka!

*Fim din ya kasance fim din Indiya da aka fi nunawa a sinima a kasar China.

*Fim din da ya kasance wanda ya fi yawan jama’a a ranar farko da aka nuna shi.

*Fim din da ya kasance wanda aka fi nunawa a karshen mako.

*Fim din kuma ya kasance wanda yafi kowane tashe.

*Ya kuma kasance fim din Indiya na farko da ya fi Chiniki a China fiye da Indiya.

An nuna fim din a fiye da gidajen sinima dubu bakwai (7000) a China, yawan gidajen sinima din da aka nuna fim din ya taimaka wajen nasarar da fim ya samu a kasar ta China.

A yanzu haka Dangal, ya samu fiye da dalar Amurka miliyan saba’in ($70M) a kasar China, fiye da dala miliyan sittin ($60) da ya samu a kasar Indiya kuma ana harsashen fim din zai samun Karin daloli na gaba.

Aamir Khan, ne fitatcen jarumi daga Indiya da yake da masoya masu dinbin yawa a kasar China, kuma shi kade ne zai iya kafa irin wannan tarihi a kasar ta China, saboda yawan masoyan da yake dasu.

Your browser doesn’t support HTML5

Aamir khan Ya Kafa Tarihi A Kasar China -3'07"