A Yau Tsohon Shugaban Catalonia Zai Bayyana Kotu a Brussels

Tsohon shugaba Catalonia Carles Pigdemont da 'yan jarida a brussels

A yau Juma’a ne ake sa ran shugaban yankin Catalonia da aka yi waje da shi Carles Pigdamont da wasu ministocinsa zasu bayyana gaban wata kotun Belgium nasaba da takardar kame ta kungiyar Tarayyar Turai da kasar Spain ta bayar.

Kotun zata saurari takaddamar a asirce daga masu shigar da kara da lauyoyin tsafaffin jami’an Cataloniar, kafin ta zartar da hukuncin mai da su kasar Spain, inda zasu huskanci shari’ar yin tawaye da tada fitina a kan rawar da suka taka wurin neman 'yancin yankin.


A watan da ya gabata ne Madrid ta bada takardar kamo Pigdemont da wasu tsofaffin ministocinsa guda hudu da suka arce zuwa Brussels ta kasar Belgium, kuma suka yi watsi da takardar sammacin bayyana gaban alkalin Spain, suna fadin cewar ba za a musu adalci ba a shari’ar.


Hukumomi a Spain sun tsige Pigdemont da majalisar ministocinsa mai wakilai goma sha uku daga ofishi a saboda yunkurin da suka yi na ganin yankin ya balle daga kasar Spain.


Yau Juma’a ne karon farko da kotun zata fara sauraren wannan karar da ake ganin zata cecekuce na cikin kotu, inda bangarorin biyu zasu iya daukaka kara a kan hukuncin kotun.