A Yau Ne Kungiyar CAN Take Fara Addu'oin Zaman Lafiya A Najeriya

Kungiyar CAN Ta Najeriya

Kungiyar hadin kan Kirista a Najeriya, wato CAN, ta shirya gudanar da addu’o’i na kwanaki uku a fadin Najeriya don rokon Allah ya kawo karshen matsalolin tsaro da kasar ke fuskanta.

Sakataren Kungiyar CAN a jihar Filato, Rabaran Polycarp Lubo yace komawa ga Allah ita ce mafita wajen magance matsalolin tsaro a Najeriya. Yace kungiyar ta dogara ga Allah ne saboda Shi kadai ne wanda zai kawo zaman lafiya a Najeriya, haka zalika makamai ba zasu ceto Najeriya ba

Shugaban majamiar ECWA na kasa da kasa, Rabaran Stephen Panya Baba yace jama'a na cike da bakin cikin kashe-kashe, satar mutane don neman kudin fansa da sauran ayyukan ta'addanci dake aukuwa a kasar.

Rabaran Panya Baba, ya bayyana matukar alhini kan yanda shugaban kasa bai canza salon yaki da yake yi da ta’addanci ba, da kuma gaza yin garanbawul a rundunar yaki da ‘yan ta’addan. Ya kuma yi kira ga mahukunta da su ba kowace kabila da kowane addini damar taka rawa a wannan yaki da ta’addanci a Najeriya.

Limamin darikar Katolika a Abuja, Arch Bishop, Ignatius Kaigama ya hori masu aikata ta'asar da su tuba. Yace idan masu aikata wadannan danyun ayyuka sun dauka babu wanda yake ganin su, toh su tuna Allah Na ganin su, dan haka su tuba su koma ga Allah su daina cutar da al’umma.

Daga jihar Filato ga karin bayani da Zainab Babaji ta aiko mana:

Your browser doesn’t support HTML5

KUNGIYAR CAN TA FARA GUDANAR DA ADDU AR ZAMAN LAFIYA