Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City a yau tana shirin karbar bakoncin
Liverpool a filin wasa na Etihad a gasar Firimiya lig mako na 21.
Wannan wasa zai ja hankalin masu sha'awar kwallon kafa a duniya, tsakanin kungiyoyi biyu wanda ke saman teburin gasar ta bana.
Wasan dai shine wasan da ake ganin zai yi tasiri sosai ga makomar kungiyoyin biyu, wanda dukkanninsu za su iya lashe kofin firimiya na kasar Ingila na shekarar 2018/2019.
Inda yanzu haka Liverpool tana da maki 54, ta ba Manchester City tazarar maki bakwai a saman teburin, wace take ta uku da maki 47, a kasan Tottenham na biyu da maki 48, don haka Manchester City za ta nemi ta rage yawan makin zuwa hudu dazarar ta doke Liverpool domin ta dawo na biyu.
A bangaren Liverpool kuwa dazarar tayi nasara a wasan ta ba City tazara maki 10, hakan kuma zai kara wa tawagar Jurgen Klopp din karfin gwiwa na lashe kofin Firimiya a karon farko.
Har yanzu dai ba'a samu nasara akan Liverpool ba acikin wasanni 20, da ta buga bangaren Firimiya lig na bana, koda a kwanan nan ta lallasa Arsenal daci 5-1.
Ita kuwa Manchester City ta jera wasanni biyu ana doke ta cikin gasar ta bana. Wasan zai gudana ne da misalin karfe Tara na yammaci Agogon Najeriya, Nijar, Kamaru da kasar Ghana.