A Yau Laraba Kristoci 'Yan Darikar Katolika Ke Fara Azumi

Papa Roma Francis

A wannan ranar ta Laraba da aka yi wa lakabi da "Ash Wednesday" wato Larabar toka, 'yan darikar katolika da wasu dariku a fadin duniya ke fara gudanar da addu'o'i da azumi na tsawon kwanaki arba'in, har zuwa lokacin tunawa da mutuwa da tashin annabi Isa Almasihu, kamar yadda suka yi imani.

Limamin dake kula da Cocin katolika da ake kira Fatima Cathedral a birnin Jos, Rabaran Fada Paul Pam, yace suna sanya alamar giciye da toka a goshinsu ne don tunatar da jama'a cewa mutum ba komai bane, shi ma wata rana zai zama toka ko kasa ya kuma koma wurin Allah.

A wannan ranar ta Laraba, kungiyar Bishop-bishop din Najeriya ta yi kira ga mabiya darikar katolika da su sanya bakaken tufafi don yin addu'o'i da rokon Allah saboda neman sauki a matsalolin tsaro da zamantakewar da Najeriya ke fuskanta.

Sir Catechist Peter Romji, wani dan darikar katolika ne da ya halarci taron, ya tabbatar da cewa addu'o'in neman zaman lafiya zasu yi a wannan lokacin na azumin kwanaki arbain.

Ga karin bayani cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

A Yau Laraba Kristoci 'Yan Darikar Katolika Ke Fara Azumi