WASHINGTON, D.C. —
A yau za'a fafata a wasan karshe na cin kofin zakarun turai Europa Cup, tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Chelsea da abokiyar hamayyarta Arsenal.
Masu fashin baki kan wasan kwallon kafa a duniya na ganin, mai horas da kungiyar Arsenal Unai Emery, zai iya sake shiga tarihi da kafar dama, kasancewar ya taba lashe wannan kofi har sau uku tare da kungiyar Sevilla, ta kasar Spain.
Inda ake ganin cewar idan har ya samu nasarar lashe kofin da tawagar Arsenal, zai dawo da martabarta cikin manyan kungiyoyi, bayan ta share shekaru 22 a karkashin jagorancin Arsene Wenger.
Wasan dai za'a buga shine a filin wasa na Baku dake kasar Azarbeidjan da misalin karfe takwas na yammaci agogon Najeriya, Nijar, Kamaru da kasar Chadi.